Mutane 19 sun mutu a wani hari da 'yan bindiga suka kai a wani kauye a Najeriya.
A jihar Niger da ke tsakiyar arewacin Najeriya, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani kauye. Maharan da suka kai hari kan fararen hula sun kashe mutane 19.
A farkon makon nan a Najeriya, mutane 16 sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a harin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.