An sanar da cewa an kai harin bindiga a wani wurin shakatawa dake jihar Wisconsin a kasar Amurka lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane uku da raunanan wasu biyu.
Jami'ai sun sanar da cewa a garin Somers dake karkashin gundumar Kenosha ne wasu yan bindiga suka kai hari da bindiga a wani filin shakatawa.
A harin mutum 3 sun rasa rayukansu inda wasu 2 suka raunana.
Kawo yanzu dai 'yan sanda basu gano wadanda suka kai harin ba amma ana cigaba da gudanar da bincike.