Sakamakon yadda zafin rana ya kai daraja 50 a ma'aunin celcius a Indiya ya sanya aka shiga yanayin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewar a cikin shekaru 10 da suka gabata ba a taba ganin yanayi irin haka ba a kasar.
Mahukunta sun bayyana cewar daga ranar Juma'ar ana sa ran yanayi ya dawo yadda aka saba gani, kuma tsananin zafin da aka gani a ranar Larabar nan a Indiya ya zama shi ne mafi tsanani a duniya a baki daya.
Sanarwar ta kuma ce guguwar Amphan da aka fuskanta a makon da ya gabata ce ta janyo tsananin zafin ranar.
A New Delhi Babban Birnin Indiya tsananin zafin ya kai daraja 47 inda a wasu jihohin kuma aka hana fita waje, sannan aka shawarci jama'a su yi ta shan ruwa.
A kasar da zafin ya tsananta akwai sama da mutane miliyan 10 da suke fama da matsalar ruwan sha.
A watannin Afrilu, Mayu da Yuni ana samu zafi sosai a Indiya, kuma a shekarar 2015 akalla mutane dubu 2,021 ne suka mutu sakamakon tsananin zafin rana da aka fuskanta a kasar.