Dai dai lokacin da kowannensu ke samun ƙarin masu dafa masa wajen ci gaba da yaƙin neman zaɓe, wani batu da ake ganin zai sake kawo wa Trump cikas bai wuce bayanan da ke nuna cewa ɗan takarar a lokuta da dama ya kan jinjinawa Adolf Hitler ba, inda hadiminsa kuma wani tsohon Janar ɗin Soja a fadar White House John Kelly ya bayyana cewa shugaban a lokacin ya na karagar mulki ya sha jinjinawa Hitler.
Sai dai alamu na nuna cewa wannan kamalai bai karya gwiwar ɗimbin magoya bayan ɗan takarar ba, musamman ganin yadda suke cikin ɗimbin Amurkawa aƙalla miliyan 38 da kawo yanzu suka kaɗa ƙuri'unsu.
Trump wanda ke samun goyon bayan galibi cikakkun Amurkawa ko a yau Talata ya sha alwashin tiso ƙeyar miliyoyin baƙi da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba a ranar farko ta shigarshi ofishi bayan nasarar lashe zaɓen.
A ɓangare guda, Kamala Harris yanzu haka na ƙoƙarin juya teburi ne wajen ganin ta samu goyon bayan baƙaƙen fata Maza waɗanda galibinsu ke mara baya ga Trump a wannan karon.
Batutuwa masu alaƙa da manufofin tattalin arziƙi da alaƙar ƙasar da ƙasashen ƙetare baya ga batun makomar baƙin haure sune batutuwan da kowanne cikin ƴan takarar ke fatan ganin ya janyo hankalin magoya bayansa da su.
Sai dai batun da ya shafi yaƙin Rasha a Ukraine da kuma rikicin gabas ta tsakiya na cikin batutuwan da ake ganin jam'iyyar Democrats za ta fuskanci koma baya ta dalilinsu.
Yanzu haka dai ana kankankan ne tsakanin Trump da Harris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI