A dai dai lokacin da aka shiga rana ta biyu da faro aikin wannan yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas, wanda ya kai ga sakin fursunonin Isra’ilan 3 a gefe guda ita kuma ta saki Falasɗinawa 90 da ta ke tsare da su, alƙaluman jami’an lafiyar yankin na Gaza sun ce ƙasar ta yahudu ta hallaka mutane fiye da dubu 47 a tsawon watanni 15 da ta shafe ta na luguden wuta kan al’ummar yankin.
A gefe guda alƙaluman sun nuna yadda ake da majinyata fiye da dubu 111 galibinsu mata da ƙananan yara, kuma kaso mai yawa na waɗannan majinyata sun rasa wani sassa na jikinsu kama daga hannu ko kafa.
Rundunar tsaron civil defence ta yankin na Gaza ta ce ta yi amannar akwai gawarwaki aƙalla dubu 10 ko fiye a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.
Hukumar agaji ta yankin na Gaza ta ce akwai gangar jikin mutane dubu 2 da 840 da suka zagwanye gabaki ɗaya kuma babu ta yadda za a iya ganowa ko kuma tattara su.
Iyalai da dama da suka koma gidajensu ba su iya gano rukunin gidajen a unguwanninsu ba sakamakon yadda Isra’ila ta shafe watanni 15 ta na yiwa yankunan luguden wuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI