Ana fargabar wajen da wani kumbo na China zai fado a duniya

Ana fargabar wajen da wani kumbo na China zai fado a duniya

Duniya ta fara shirin ko ta kwana bayan firgitar da aka samu sakamakon kaucewa hanyarsa da wani kumbo na China mai suna Long March 5B ya yi a sama.

Kakakin Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Amurka Mice Howard ya bayyana cewa, a ranar 8 ga Mayu ne suke sa ran kumbon zai sauka a duniyar sama, kuma Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Amurka ta bibiye shi.

Howard ya ce, a yanzu ba a san a wanne bangare na duniya bangarorin kumbon za su fado ba, kuma sai ya rage 'yan awanni kafin fadowar sannan za a iya hasashen hakan.

A makon da ya gabata ne China ta harba taurarin dan adam da kumbon zuwa sama.

An bayyana cewa, bayan kumbon ya kaucewa hanyarsa, wasu bangarorinsa sun kone a sama, ana fargabar wasu bangarorin kumbon mai nauyin tan 22 za su fado duniya.


News Source:   ()