Da farko dai mutane 14 ne wata majiyar tsaro daga yankin ta tabbatar wa Kamfanin Dillancin Laraban Faransa AFP mutuwarsu, kafin daga bisani rahotanni su nuna cewa adadin ya ƙaru.
Wani babban jami’in yankin Francois-Xavier Bieuville, ya bayyana cewar akwai yuwar daruruwan mutane ne suka rasa ransu a sanadiyar guguwar, duk da cewa abu ne mai wuya a iya ƙididdige adadin waɗanda suka mutu, sakamakon mafi akasarin mazauna yankin Musulmi ne da bisa al’ada suke gudanar da jana’iza da wuri.
Tuni dai babbar jami’ar ƙungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta buƙaci kaiwa al’ummar yankin ɗaukin kayan agaji, inda ta ce a shirye suke su aike da nasu a cikin kwanaki masu zuwa.
Kawo yanzu dai akwai jirage biyu na sojoji daga La Reunion, wani tsibiri shima mallakin Faransa da ya kai kayan agaji na magani tan uku da jami’an kiwon lafiya 17, kuma a yau ne ake saran isowar wani jirgin ruwa shima ɗauke da kayan agaji daga yankin.
Ana saran ministan harkokin cikin gidan Faransa Bruno Retailleau a yau ya ziyarci yankin tare da sojoji 160, ƙari kan 110 da aka fara aikewa tsibirin.
Lalacewar da tashar jiragen saman tsibirin na Mayotte yayi sanadiyar guguwar ta Chido da kuma katsewar wutar lantarki, ya ƙara sanya wahala a ayyukan jin kai a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI