Ana fargabar kara yaduwar Covid-19 a Siriya

Ana fargabar kara yaduwar Covid-19 a Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta fadakar da cewa akwai yiwuwar kwayar cutar corona ta kara yaduwa a kasar Siriya. 

Mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya  ya shaidawa manema labarai cewa,

"Akwai fargabar Covid-19 ka iya kara yaduwa a kasar Siriya "

Ya kara da cewa a yankin da ke hannun kulawar gwamnatin kasar kwayar cutar corona ta yi ajalin mutane 21 inda yawan wadanda suka kamu ya haura 439.

Ya yi sharhin cewa duk da a kasar akwai karancin wadanda ke dauke da cutar idan aka kwatanta da sauran kasashe, akwai yiwuwar kwayar cutar ta kara yaduwa a kasar. 

 


News Source:   www.trt.net.tr