An sanar da cewa an kashe 76 daga cikin gobarar daji sama da 100 a jihohi 18 a Aljeriya.
A cewar rubutacciyar sanarwa da kungiyar kare fararen hula ta Aljeriya ta fitar, an kashe dukkan gobarar 40 a lardin Tizi Vizu, wadda ita ce cibiyar gobarar daji a kasar.
An bayyana cewa an kashe gobara 76 daga sama da 100 na gandun daji a cikin kasar kuma ana ci gaba da ayyukan sanyaya yankin, kuma an gargadi mutanen da ke zaune a kusa da wuraren kashe gobarar da su “yi taka -tsantsan a yayin da ake fama da zafin yanayi”.
Sanarwar ta kuma lura cewa ana ci gaba da kashe wutar gobara 35 a jihohi 11.
Mutane 69 da suka hada da sojoji 28 da fararen hula 41 sun mutu a gobarar daji a jihohi 18 na kasar.
Shugaban kasar Aljeriya Abdulmajid Tebboune ya sanar da cewa an tsare mutane 22 da ake zargi da yin zagon kasa sannan ya ce, "Wadanda ake zargi ne suka haddasa gobarar."