A Isra'ial dubun dubatan al'umma sun gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar gwamnatin kasar akan rikon sakainar kashin da tafkin cin hancin da rashawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu ke aikatawa.
Jaridar Haaretz ta yada a shafinsa ta yanar gizo da cewa, tun daga Kudus har zuwa tel Aviv a gurare kusan 260 an gudanar da zanga-zanga domin kira ga shugaba Netinyahu ya yi murabus.
Hukumar Yada Labaran Kasar Isra'ila (KAN) ta sanar da cewa dubun dubatan al'umma sun taro domin gudanar da zanga-zanga a gaban gidan gwamnatin kasar.
An dai kwashe watanni biyu kenan ana kira da firaiministan Netanyahu ya yi murabus.