Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa ana ci gaba da samun kasa da mutum 1,000 daga cikin masu kamuwa da cutar corona a kasar Turkiyya a ko wace rana.
Sai dai an samu karuwa da kamuwa da cutar a garuruwan Ankara, Mardin, Diyarbakir, Gaziantep da Konya.
A ranar 1 ga watan Agusta marasa lafiya 981 aka samu sun warke inda yawan ya dan kasa daga wadanda aka samu da cutar a ranar.
A bisa haka a ranar Asabar daga cikin mutum dubu 44, 846 da aka yiwa gwajin kwayar cutar ta Corona an samu mutum 981 sun warke inda kuma aka samu mutum 996 dauke da ita.
Kawo yanzu dai a fadin kasar Turkiyya an yiwa mutum miliyan 4,845,669 gwajin kwayar cutar ta Covid-19, daga cikinsu an samu dubu 231,869 dauke da cutar, daga cikin wadanda ke dauke da cutar dubu 215,516 sun warke inda kuma dubu 5,710 suka rigamu gidan gaskiya