Ana ci gaba da neman mutane rana ta 5 bayan ambaliyar ruwa da zaftarewar kasar da suka afku a Japan tare da yin ajalin mutane 7.
A kalla gidaje 130 ne suka rushe sakamakon ibtila'in da ya afku a garin Atami na jihar Shizuoka da ke kudu maso yammacin Tokyo babban birnin Japan a ranar 3 ga Yuli.
A aiyukan neman jama'a da ake ci gaba da yi a garin an gano karin gawarwakin mutane 3 wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa mutane 7.
Ana tunanin sama da mutane 20 ne suka bata sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da suka afku a garin.
Jami'an ceto da suka hada da na 'yan sanda, kwana-kwana, sojoji da na jin kai na kokarin ciro mutane daga karkashin kasa a garin na Atami.