Ana ci gaba da magance 'yan ta'adda a yankunan Iraki

Ana ci gaba da magance 'yan ta'adda a yankunan Iraki

Rundunar sojan Turkiyya ta kai farmaki a yankin Beytushebap  dake Iraki inda ta yi nasarar magance 'yan ta'addar PKK biyu.

Dangane ga bayanan da suka fito daga ma'aikatar cikin gida dakarun kasar sun kaddamar da farmakan kalubalantar ta'addanci da hadin gwiwar jami'an sojin sama.

A farmakan da aka yi amfani da jirage marasa matuka an yi nasarar kashe 'yan ta'adda 2. Ana kuma ci gaba da yaki da ta'addanci ba tare da gajiwa ba.

A dayan barayin kuma ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta bayyana cewa,

Domin dakile hare-haren ta'addancin da 'yan ta'addar PKK ke kaiwa an kaddamar da farmakai inda aka magance dan ta'adda 1 a yankin Farmakin Garkuwar Firat da kuma kame 'yan ta'addar PKK/YPG 6 a yankin da aka kaddamar da Farmakin Reshen Zaitun.

 


News Source:   www.trt.net.tr