A kasar Japan an zubar da allurar riga-kafin Korona samfarin Pfizer-BioNTech fiye da kwara dubu saboda katsewar wutar lantarki daga naurorin dake sanyayasu.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran NHK ta rawaito a daya daga cikin ma'aikatun da aka adana allurar rigakafin an samu katsewar wutar lantarki sabili da wata yar matsala.
Sabili da katsewar wutar lantarki allurar rigakafin korona 1032 sun kasance cikin rashin sanyin da ake bukata lamarin da ya haifar da lalacewarsu.
Da aka gudanar da bincike an gano cewa firjin da aka sanya a soket din wuta daya ya haifar da nauyin da wutar soket din ta dauke lamarin da ya haifar da tsayawar aikin dukkanin firij din abinda ya sanya lalacewar allurar rigakafin.