Da fari a zagayen farko kuri’u 71 Joseph Aoun ya samu, daga bisani kuma ya samu kuri’u 99 daga cikin 128 da ‘yan majalisar suka kaɗa duka a yau, yayin zaman da ya samu halartar wakilan ƙasashe da dama ciki har da jakadan Faransa a kasar ta Lebanon Jean Yves Le Drian, da kuma wakilan Amurka da Saudiya, ƙasashen da suka marawa takarar Joesph Aoun ɗin baya.
Tun bayan karewar wa'adin tsohon shugaba Michel Aoun a watan Oktoban 2022, majalisar majalisar Lebanon ta gaza zaɓar sabon shugaba sai a wannan karon, abinda ya sa masu sukar Hezbollah zargin cewa kungiyar ce ta hana zaben da gangan da zummar neman ɗora ɗan takararta Suleiman Frangieh. Sai dai a jiya Larabar ya sanar da janye takararsa atre da marawa Janar Joseph Aoun baya.
Ana dai kyautata zaton cewar, muhimmiyar rawar da sojojin Lebanon suka taka wajen ƙullawa da kuma aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah da ta fara aiki a ranar 27 ga watan Nuwamba ce taimakawa sabon shugaba Joseph Aoun ɗarewa kujerar shugabancin kasar.
A karkashin tsarin shugabancin da Lebanon ke bi tun bayan kawo ƙarshen yakin basasar ƙasar da aka gwabza tsakanin shekarar 1975 zuwa 1990, Kirista ke riƙe muƙamin shugaban kasa, yayin da Sunni ke zama Fira Minista, sai kuma mabiyin Shi’a a matsayin kakakin majalisar dokoki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI