An zabi dan kasar Chadi Taha a matsayin Sakatare Janar na Tarayyar Kasashen Musulmi (OIC)

An zabi dan kasar Chadi Taha a matsayin Sakatare Janar na Tarayyar Kasashen Musulmi (OIC)

An zabi dan kasar Chadi Hussaini Ibrahim Taha a matsayin Sakatare Janar na Tarayyar Kasashen Musulmi (OIC).

A taron kolin ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar da aka gudanar karo na 47 a Niamey babban birnin Nijer ne aka zabi wanda zai maye gurbin Sakate Janar din OIC wanda ke kan gado Yusuf Bin Al-Useymin wanda wa'adin mulkinsa zai kare a watan Nuwamban shekarar 2021.

An dai amince da dan kasar Chadin Hussaini Ibrahim Taha ya zama Sakatare Janar na Kungiyar Tarayyar Kasashen Musulmi (OIC) na 12.

Sakatare Janar Useymin ya janye daga takararsa inda Benin da Nijeriya suka goyawa dan takarar daga Chadi baya.

 


News Source:   ()