An sanar da yiwa shugaban kasar Kazakhistan Kasim Comert Tokayev allurar riga-kafin Korona samfarin Spunik V.
Mai magana da yawun shugaban kasar Kazakhistan Berik Uali ya yada a kafafen sadar da zumunta da cewa bayan yiwa shugaba Tokayev allurar rigakafin Korona ya kasance cikin koshin lafiya.
Uali, ya kara da cewa Tokayev ya bayar da umarnin yiwa dinbin alumman kasar allurar rigakafin Spunik V da kasar Rasha ta sarrafa.
Inda ya kara da cewa "Shugaban kasa na kira ga dukkanin al'umman kasar su garzaya domin yin allurar rigakafin Korona"