A kasa Serbia an yiwa kashi 50 na manya mutane allurar rigakafin sabon nau'in cutar coronavirus (Kovid-19).
Firaimistan Serbia Ana Brnabic ta sanar a wani taron manema labarai cewa an yiwa rabin mutanen da suka balaga a kasar allurar rigakafin korona.
Da ta ke bayyana cewa wannan adadi bai isa ba don samun garkuwar jiki, Brnabic ta ce, "Akwai isassun alluran rigakafi a Serbia da za'a iya yiwa alumma har sau uku."
Brnabic ta ce allurar rigakafin da kamfanin samar da magunguna na Amurka wato Moderna ya samar zai isa zuwa kasar a karshen kwata na 2021.
A Serbia, mutane dubu 7 da dari 132 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar.
A cikin kasar da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar har 579 a cikin awanni 24 da suka gabata, mutane 724 da dubu 97 ne aka gano sun kamu da cutar Kovid-19 tun farkon barkewar cutar a kasar.