An yiwa mutum biliyan 3.79 allurar riga-kafin Korona a fadin duniya

An yiwa mutum biliyan 3.79 allurar riga-kafin Korona a fadin duniya

Kididdigar allurar rigakafin COVID-19 da aka gudanar a duk faɗin duniya ya haura biliyan 3.79 a cewar shafin yanar gizon Jami'ar Oxford ta ourworldindata.org.

Kasar China, inda cutar ta fara bulla a karshen shekarar 2019, ita ce ta farko a duniya, da yin rigakafin  sama da biliyan 1.51 a cikin kasar, sai kuma Indiya da ke biye da kusan miliyan 423.4.

Amurka ta ayyanar da sama da miliyan 339.7, sannan Brazil ta biyo baya da sama da miliyan 130.

A  Jamus an yi allurar riga-kafin Korona (miliyan 88.4), Birtaniya (miliyan 83.2) da Japan (miliyan 73.9).

Kawo yanzu Turkiyya ta yi allurar rigakafi sama da miliyan 64.8, wanda hakan ya sanya ta zama ta tara a duk duniya, haka kuma  sama da mutane miliyan 39.2 suka karbi a kalla kashi daya na allurar.


News Source:   ()