An yiwa jariri dan watanni 8 a allurar riga-kafin Corona a Amurka

An yiwa jariri dan watanni 8 a allurar riga-kafin Corona a Amurka

A jihar New York ta Amurka an yiwa wani jariri dan watanni 8 allurar riga-kafin Corona (Covid-19) ta Pfizer/BioNTech.

Jaririn mai suna Enzo Mincolla ne mutum mafi karancin shekaru a duniya da aka yiwa allurar riga-kafin Corona.

An yiwa Mincolla allurar da amincewar iyayensa a wani bangare na aiyukan gwaji da asibitin jihar New York yake gudanarwa.

An bayyana cewa, jaririn da iyayensa likitoci ne, bai nuna alamun wata matsala ba, kuma yana nan kalau da shi.

Mahaifin jaririn Mike Mincello ya sanar da cewa, game da yin allurar riga-kafin Corona tun daga lokacin da aka fara gwaji na farko zuwa yau yana sanya idanu sosai kuma bai taba samun wani taraddudi ba.

Mahaifiyar jaririn Anne Marissa Mincolla kuma ta bayyana cewa, aminci da allurar ke da shi zai zama abun misali ga sauran iyaye.


News Source:   ()