An yiwa firaiministan Hungary Victor Orban allurar riga-kafin korona sanfarin Sinopharm da kasar China ta sarrafa.
Orban, ya bayyana cewa ya kamata ko wani jami'in gwamnatin kasar ya karbi allurar riga-kafin inda ya bayyana cewa shi ma an yi masa allurar ta China.
Bayan yi masa allurar, Orban ya bayyana cewa ya kara jin karfin jikinsa, inda ya yi kira ga al'umman kasar da su je domin yi musu allurar riga-kafin Koronar.