An zargi wasu da yin kutse kan kundin adana bayanan Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Tashar Fox News da ke Amurka ta bayyana cewa, an yi kutse ga Ma'aikatar Harkokin Wajen Kasar, an kuma bayar da sanarwar yiwuwar aikata hakan ga Ma'aikatar Tsaro.
A labaran an bayyana cewa, an yi kutsen makonni 2 da suka gabata.
Wani jami'an Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da ya yi bayani ga tashar Fox News ya shaida cewa, saboda dalilai na tsaro a yanzu ba za su iya bayar da wani bayani game da batun kutsen ba.