A Vienna Babban Birnin Kasar Ostiriya an gudanar da zanga-zangar la'antar kisan bakar fata Ba'amurka George Floyd da 'yan sandan Amurka suka yi bayan kama shi.
Kusan mutane dubu 5 ne suka taru a dandalin Hakkokşn Dan Adam na Ostiriya inda suka daga allunan da aka rubuta "Ba na iya numfashi", A daina zalunci, a zauna da juna", "Akwai nuna wariya a Ostiriya kuma a hada kai a yanki zaluncin da 'yan sanda ke yi".
Masu zanga-zanga sun kuma rufe manyan hanyoyin birnin inda suka yi tattaki zuwa Dandalin Karls.
A jawaban da aka yi a Dandalin an mayar da martani game da nuna wariya da ake yi a nahiyar Turai. Masu jawabai sun ja hankali kan yadda 'yan sanda ke amfani da karfin da ya wuce ka'ida, sun kuma yi kira da a kare muradun mtane marasa rinjaye da ke Yammacin Duniya wadanda suke fuskantar nuna wariya.
A ranar 25 ga watan Mayu ne 'yan sandan Amurka suka kama wani bakar fata George Floyd wanda ya dinga ihun "Ba na iya numfashi" amma duk da haka suka shake shi tare da kashe shi.
Tun daga wannan rana zuwa yau ake ta tayar da zaune tsaye a Amurka inda ake la'antar amfani da karfi da ya wuce ka'ida da 'yan sandan kasar ke yi.