Daruruwan mutane a kasar Ajantina sun gudanar da zanga-zanga tare da la'antar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Falasdinawa.
Mutanen sun taru a wani waje dake kusa da ofishin jakadancin Isra'ila a Boenos Aires babban birnin Ajantina tare yin tofin Allah tsine ga Isra'ila.
Mutanen sun bayyana hare-haren na Isra'ila, kasar masu nuna wariya da nuna fifikon Yahudawa a matsayin kisan kare dangi.
Masu zanga-zamgar sun dinga daga allunan da aka rubuta "Isra'ila na yiwa Falasdinawa abunda Nazi ta yi musu." da "Nazi ta yi a lokacin babu kasar Isra'ila, Falasdin za ta samu 'yanci".
Daga baya masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa Obelisco dake tsakiyar birnin.