A Vienna Babban Birnin kasar Ostiriya, an gudanar da zanga-zangar adawa da Isra'ila bisa irin yadda ta ke zaluntar Falasdinawa, da kuma Amurka da ke goya mata baya.
Masu zanga-zangar sun taru a gaban Ofishin Jakadancin Amurka da ke Vienna, sun dinga daga allunan da aka rubuta "A daina mamayar yankunan Falasdinawa", "Ostiriya, Isra'ila da Amka su daina goyon bayan mulkin danniya" da "A kauracewa Isra'ila".
A jawaban da aka yi a wajen zanga-zangar an sake mayar da martani tare da la'antar yunkurin Isra'ila na sake mamye wasu yankunan Falasdinawa da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan, an kuma nuna bukatar da a yi aiki da yarjejeniyar 1967 matukar ana so a samu zaman lafiya a yankin.
Masu jawabi a wajen sun bukaci Ostiriya da Jamus da su janye shirin hadin kai da Isra'ila wajen tsaro a yanar gizo, kuma su janye kokarin sayen wasu kayayyaki daga kasar.
Da yake jawabi a wajen, pasto Franz Sieder ya ce a matsayinsa na malamin addini yana neman a bayar da kariya ga mutanen da ake zalunta don a samar da zaman lafiya, kuma Falasdinawa ne ake zalunta a rikicin da ake yi tsakanin Falasdin da Ira'ila.