An yi yunkurin kashe wani mashahurin dan jaridar kasar Holland

An yi yunkurin kashe wani mashahurin dan jaridar kasar Holland

Mashahurin dan jaridar kasar Holland Peter R. de Vries ya fuskanci harin 'yan bindiga inda yake cikin halin rai mutu kwakwai. An kama mutane 3 game da harin.

An samu labarin cewa, an kai harin a Amsterdam babban birnin Holland inda aka harbe shi a kansa.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sun ji karar harbi sau 5.

An kai dan jaridar asibiti da ke cikin mawuyacin hali, 'yan sanda kuma sun bayyana kama mutane 3.

Firaministan Holland Rutte ya ce, lamarin na da ban tsoro da sosa zuciya.

Dan jaridar na kasar Holland mai shekaru 64 ya shahara da gudanar da bincike kan kungiyoyin mafiya.

An bayyana cewa, yana yawan fuskantar barazana a saboda haka 'yan sanda sun taba ba shi kariya.


News Source:   ()