A shekarar 2019 da ta gabata an yi wa yara kanana sama da dubu 23 allurar riga-kafin cututtuka a Yaman.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) na Yaman ta bayyana cewar tare da taimakon da kasar Kuwait ta bayar an yi wa Yamanawa 'yan kasa da shekaru 5 su dubu 23,433 allurar riga-kafi a shekarar 2019.
Sanarwar ta ce rikicin Yaman ya shafi yara kanana da ba su da karfi, kuma Kungiyar na yin duk mai yiwuwa don kare yara kanana.
A farkon watan Mayu WHO ta yi gargadi game da Yaman inda ta ce tsarin kula da lafiya na kasar ya ruguje baki daya, kuma akwai yiwuwar cutar Corona (Covid-19) ta kama sama da rabin jama'ar kasar.