An yi taron ibada na farko a Notre Dame cikin shekaru 5

An yi taron ibada na farko a Notre Dame cikin shekaru 5

Archbishop Lauren Ulrich ne ya jagoranci aƙalla mutane dubu 2 da 500 da suka ƙunshi shugabannin ƙasashe daban daban ciki har da mai masaukin baƙi wato Emmanuel Macron na Faransa, wajen gudanar da taron Ibadar na farko a Mujami’ar ta Notre Dame, wadda aka shafe shekaru biyar ana aikin sake gina ta a birnin Paris.

Sai dai shugaba Macron ya ƙi karɓar Jibii, la’akari da cewar gwamnatin Faransa ba ta alaƙanta kanta da addini.

Ƙididdiga ta nuna cewar aƙalla mutane miliyan 12 ke ziyartar Mujami’ar Notre Dame a duk shekara, amma bayan sake gina ta da aka yi, ana sa ran adadin masu ziyarar ya ƙaru zuwa mutane miliyan 15 duk shekara.

A ranar 16 ga watan Disambar nan ake sa ran bai wa mutane gama gari damar damar fara ziyartar Notre Dame don Ibada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)