Masana ilmin sararin samaniyya sun yi nasarar daukar ainihin hoton duniyar Jupiter ta amfani da dabarar da aka sani da "hoto mai sa'a" a Maunakea Volcano dake Hawaii.
Dangane ga labaran da TechExplorist suka yada tawagar masana ilimin sararin samaniya da Michael Wong dake jami'ar California ke jagoranta karkashin Hukumar Hubble da Hukumar Ilimin Sararin Samaniya ta NASA sun yi nasarar harhada hotunan tauraron dan adam na Jano da ya yi nasarar gano duniyar Jupiter.
A wannan tsarin da aka yi amfani dashi mai taken "hoto mai sa'a" an yi nasarar daukar hoton duniya mafi girma inda aka ga tana tattare da mahaukaciyar guguwa, tamabari ja da tambarin baki da kuma walkiya.
Hoton ya nuna cewa bakin tambarin da aka gani tamkar kurwa ne na giragizai.
An yada cikekken wannan binciken a Mujalar "The Astrophysical Journal Supplement Series".