Tashar talabijin ta ABC ce ta Amurka ta shirya wannan muhawarar gabanin zaɓen ranar 5 ga watan Nuwamba, ranar da Amurkawa za su zaɓi wanda zai jagorance shi a matsayin shugaban ƙasa.
Kazalika tsohon shugaban na Amurka ya caccaki fitacciyar mawaƙiyar nan Taylor Swift saboda yadda ta nuna goyan bayanta ga Harris jim kaɗan da kammala zazzafar muhawarar.
Sai dai ƙorafin na Trump na cewa an yi masa maguɗi, babu alamun gaskiya a cikinsa, lura da rashin gabatar da hujja kan zargin da yake yi wa ƴan jaridar da suka jagoranci muhawarar.
Shiryayyen maguɗi ne, da ma na yi zaton hakan zai faru saboda idan ka duba, za ka ga cewa, suna yin gyara kan komai, amma ita ba sa yi mata gyara.
An tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin Trump da Harris
A safiyar yau ne aka tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin ƴan takarar shugabancin Amurka Kamala Harris ta jam’iyar Democrat da kuma Donald Trump na jam’iyar Republican.Khamis Saleh ya bibiyi yadda muhawar ta gudana, ga kuma rahoton da ya hada mana.
Trump da Harris a yayin tafka muhawara REUTERS - Brian SnyderTrump ya yi kakkausar suka ga salon da Democrat ta yi amfani da shi wajen tunƙarar rikicin gabas ta tsakiya ya na mai cewa idan har da shi ne akan mulki ko shakka babu yaƙin da faruwa a Gaza ba zai taɓa faruwa ba.
A ɓangare guda Harris ta bayyana shirinta na samar da ƙasashe biyu da nufin warware rikicin tsawon shekaru tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.
Dukkaninsu sun caccaki juna game da yadda Amurka ta tunƙari yaƙi da Taliban, inda Harris ta ce Trump ya tafka abin kunya bayan zaman tattaunawa da wakilcin mayaƙan na Taliban daga Afghanistan yayinda shi kuma soki gwamnatin Democrat kan yadda ta gaza cika alƙawarin kwashe Amurkawan da ke Ƙabul bayan Taliban ta ƙwace mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI