Ministan harkokin wajen Falasdin Riyad al-Maliki ya yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) da ta kakaba wa Isra'ila takunkumin sayen makamai.
Da yake jawabi ga hukumar ta UNSC a taro karo na uku don tattauna batun tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinu da hare-haren sama da ake kaiwa Gaza, Maliki ya ce ba za'a iya bayyana kalaman da mutanen Falasdinu suka jimre wa ba.
Ya bayyana cewa Isra’ila ta aikata “laifukan yaki da cin zarafin bil adama”, Maliki ya kuma tunatar da cewa UNSC na da damar da za ta kakkabawa Isra'ila takunkumi da haramta siyar mata da makamai, lamarin da zai kawo karshen irin cin zarafin da take yiwa Falasdinawa.
Haka kuma Riyad al-Maliki ga mambobin majalisar ya yi kira garesu kamar haka:
"Me ya sa ba za ku sa kanku a wurinmu ba? Me za ku yi idan kasarku tana cikin mamaya, idan an tsananta wa jama'arku da kisan kiyashi? Me za ku yi don 'yancinku, don kawo karshen fitinar?"
Tare da jaddada cewa 'yancin Falasdinu ita ce kadai hanyar zuwa zaman lafiya, Maliki ya yi kira ga Hukumar UNSC da ta dauki mataki don sauke wannan nauyin wacan nan dokar da ta rataya a wuyarta.
A halin yanzu, a bayanin da Tarayyar Kasashen Musulmi ta (OIC) ta yi,
"Idan Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ba ta dauki nauyin dakatar da cin zarafin da Isra'ila ke yiwa Falasduin ba, za ta nemi izinin Majalisar Dinkin Duniya don kare al'ummar Falasdinu."