An yi ikirarin kashe sojoji 40 a Myammar

An yi ikirarin kashe sojoji 40 a Myammar

An yi ikirarin kashe a kalla sojoji 40 sakamakon arangamar da aka yi tsakanin sojojin Myammar da kungiyoyi masu dauke da makamai dake adawa da juyin mulki.

Sanarwar da Kungiyar PDF da aka kafa bayan fara zanga-zangar adawa da juyin mulkin a ranar 5 ga Mayu ta bayyana cewa, a tsakanin 2 da 4 ga Yuli a yankin Sagaing an samu arangama a lokacin da sojojin Myammar suka kaiwa fararen hula hari.

Sanarwar ta ce, mayakan PDF sun kashe a kalla sojojin Myammar 40 tare da ragargaza motocin yaki na sojoji guda 3.

Gwamnatin Myammar ba ta ce komai ba game da batun.

 


News Source:   ()