An kame mutum uku a arangamar da magoya baya da masu adawa da tsohon shugaban kasar Amurka suka yi a birnin New York.
Kungiyar "Black Lives Matter" sun kalubalanci kafa tutar nuna wariya da wasu kungiya masu tsatsaurar ra'ayi dake nuna goyon baya ga tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump suka yi.
An yi dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin biyu lamarin da ya haifar da hatsainiya tsakaninsu.
'Yan sanda sun bayyana kame mutum uku daga cikinsu.
An kwashi artabu tsakanin magoya bayan Trump da masu adawa dashi a dandalin Times da ke birnin New York.