Hukumar Kare Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) ta yi gargadi game da dumamar da duniya ke yi wanda hatsari ne babba ga bil'adama.
Sanarwar da UNEP ta fitar ta ce, duk da hasashen da aka yi na cewar sakamakon annobar Corona (Covid-19) za a samu ragi da kaso 7 na fitar da iskar carbon a duniya, amma kuma yanayi na ci gaba da dumama wanda zai kai har sama da karin daraja 3.
Sanarwar ta ce, idan kasashen duniya suka cika alkawarin da suka dauka game da Yarjejeniyar Paris, to za a iya tsayar da dumamar duniya kan daraja 2 kawai, kuma don tabbatar da hakan dole ne a kara yawan zuba jarin da ake da shi wajen kare muhalli.
Sanarwar ta rawaito Daraktan UNEP Inger Andersen na cewa "Shekarar 2020 ta zama daya daga cikin shekaru mafiya ganin dumamar yanayi, ana ta samun gobarar daji, guguwa da fari a yankuna da dama."
A rahoton da Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya ta fitar a makon da ya gabata ta ce, shekarar 2020 ta zama shekara ta 3 bayan 2016 da 2019 wajen ganin munin dumamar yanayi a ban kasa.