A harin da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta shirya a arewa maso gabashin Najeriya, kasar dake Afirka ta Yamma, mutane 18 suka rasa rayukansu sannan mutane 21 suka jikkata.
Hakanan kuma an kashe 'yan ta'adda da yawa a farmakan da aka gudanar bayan harin.
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ziyarci yankin Damasak bayan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai.
Zulum ya ce mutane 18 sun rasa rayukansu sannan mutane 21 sun jikkata a harin.
A gefe guda kuma, Kakakin rundunar sojin Najeriya Muhammed Yerima ya sanar da cewa sojojin sun gudanar da atisayen sama da kasa kan Boko Haram a yankin Mobbar na jihar Borno.
Yerima ya bayyana cewa an kashe ‘yan Boko Haram da yawa a cikin samamen kuma an rusa mafakar‘ yan ta’addan.
A Najeriya, sama da mutane dubu 20 ne suka mutu a ta'addancin da kungiyar Boko Haram ta shirya tun daga shekarar 2009.