A farmakin da aka kai yankin da aka kaddamar da Faramakin Tafkin Zaman Lafiya dake Siriya an magance mambobin kungiyar ta'addar PKK/YPG har su biyar.
Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da cewa a yankin da aka Kaddamar da Farmakin Tafkin Zaman Lafiya a Siriya an magance 'yan ta'addan PKK/YPG 5.
Dangane ga bayanan da aka samo daga hukumomin tsaron kasar mambobin kungiyar ta'addar PYD/YPG/PKK sun yi yunkurin kutsawa a kauyukan Saida da Muallak dake karkashin Tal Abyad ta amfani da babban titin M4.
Bayan gano 'yan ta'addan an yi dauki ba dadi tsakanin Sojojin Siriya da 'yan ta'addan.
Kamar yadda hukumomin tsaron suka sanar an yi dauki ba dadin ne a yankunan Ayn Isa da kuma yankunan Tal Abyad da aka kaddamar da Framakin Tafkin Zaman Lafiya.