Wani soja ya mutu a wani artabu da aka kwasa tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro a lardin Balochistan a kasar Pakistan.
Bangaren hulda da jama'a na rundunar sojan Pakistan (ISPR) ya sanar da cewa an yi artabu tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'adda a yankin Karan na Balochistan.
Yayin da aka kashe 'yan ta'adda 2 a rikicin, wani soja ya rasa ransa.
Sanarwar ba ta bayar da wani bayani game da kungiyar da 'yan ta'addar suke ba.