A harin da aka kai kan ayarin fararen hula da jami'an tsaro a yankin Sahel na Burkina Faso, mutane 47 sun rasa rayukansu yayin da akalla 19 suka jikkata.
An kai harin ne kan jerin gwanon motocin da ke dauke da sojoji da jami'an tsaro na sa kai a yankin Gorgadji na gundumar Soum.
A harin, fararen hula 30, jami'an tsaro 14 da masu aikin sa kai 3 da suke taimakawa jami'an tsaron sun rasa rayukansu.
Bayan harin, wanda akalla mutane 19 suka jikkata, an bayar da rahoton cewa jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda 58 a martanin da suka mayar.
Kungiyoyin ta'addanci masu alaka da Al-Qaeda da Daesh da ke aiki a makwabciyar kasar Mali suna kai hare-hare akai-akai a arewa da gabashin Burkina Faso tun daga shekarar 2015.
Duk da cewa Burkina Faso tana gudanar da ayyukan soji na hadin gwiwa da Nijar makwabciyarta a Sahel, amma ba za ta iya raunana karfin kungiyoyin 'yan ta'adda da ke jibge a Mali ba.
Dangane da bayanan Majalisar Dinkin Duniya, mutane 17,500 ne suka bar kasar saboda dalilan tsaro tun farkon shekarar bana.