A kasar Iran an yankewa editan wata jarida mai suna Ruhullah Zem dake adawa da gwamnatin kasar hukuncin kisa da laifin "aikata barna a doron kasa".
Mai magana da yawun kotun kasar Gulam Hüseyin İsmaili ya yiwa 'yan jarida bayani a Tahran babban birnin kasar game da shari'ar Zem editan jaridan "Amednews" mai adawa da gwamnatin kasar.
Ya bayyana cewa a yayinda ada kama Zem da laifuka 13 ya cancanci hukuncin kisa sauran 'yan jaridun da aka kama da wasu laifuka kuma an tasa kyeyarsu zuwa gidan wakafi.
Jaridar Amednews ta fara ayyukan gwagwarmaya, fadakarwa akan demokradiyya ta shafukan sanar da zumunta tun a shekarar 2015.
A cikin dan kankanen lokaci ta samu mabiya fiye da miliyan daya an kuma an rufeta bayan shekaru biyu lamarin da ya sanya Zem cigaba da gwagarmaya a matsayin Sedaimardom 'Sautin al'umma'. An dai kama shi a watan Oktoban shekarar 2019.