Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 ga mutumin da tayar da gobara tare da kashe mutane 6 da suka hada da Turkawa 4 a shekarar 2017 a garin Malhouse na Faransa.
Babbar Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Colmar ta yanke hukuncin game da tayar da gobara tare da kashe Turkawa 4 daga iyalan Ertunc da Aksu dakuma wasu 'yan asalin Aljeriya 2 da aka yi a unguwar Bourtzwillerda ke garin Malhouse a ranar 1 ga Oktoban 2017.
Kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari ga dan kasar Faransa Aurelien Roellinger da aka samu da laifin kashe mutanen.
Lauyar Turkawa Gulcan Yasin ta ce,
"Wadanda suka mutu ba za su dawo ba, amma an yi adalci a shari'ar."