Tun gabanin yau Litinin anga wani yanayi da ba safai aka saba gani a Amurka ba, wato girke jami’an tsaro a kaso mai yawa na jihohin ƙasar saboda fargabar tarzoma ciki kuwa har da birnin Washington fadar gwamnati da kuma Oregon inda aka samu tarzoma a wancan zaɓen da ya gabata.
Yayin kaɗa ƙuri’ar da masu zaɓen wuri suka yi a Amurkan an ga yadda aka cinna wuta a akwatuna har guda 3 a Vancouver da Washington da ya kai ga lalata tarin ƙuri’u batun da ake ganin na daga cikin dalilan da suka sanya girke jami’an tsaron.
Bugu da ƙari an ga tashin tarzoma yayin kaɗa ƙuri’un na wuri a Portland da Oregon da ya kai ga cinna wuta a mabanbantan wurare.
Babu dai cikakkun alƙaluma kan yawan dakarun da aka girke a sassan na Amurka sai dai ma’aikatar tsaron cikin gida ta ce ta samu barazana game da yiwuwar tayar da tarzoma ko kuma lalata kayakin zaɓe.
Wannan shi ne zaɓe mafi ɗaukar zafi da Amurka ta gani a tarihi lura da irin kalaman muzanta juna da ke ci gaba da fita tsakanin ƴan takarar jam’iyyun biyu tal da ke mulki a ƙasar mafi ƙarfin demokraɗiyya.
Bayan zaɓen 2020 an ga yadda tarzoma ta tashi tare da haddasa asarar rayuka ciki har da na jami’an tsaron Capitol.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI