An tono zuciyar magajin garin Verviers na farko a Beljiyon

An tono zuciyar magajin garin Verviers na farko a Beljiyon

An sanar da cewa a yayin aikin gyaran maɓuɓɓugar ruwa a garın Verviers dake Belgium an tono 'zuciyar' magajin garin na farko.

Ma'aikatan ma'aikatan ruwan kasar Beljiyon suka bayyana sun tono zuciyar magajin garin a ranar 20 ga watan Agusta daya rasu a shekarar 1839.

An sarkahe zuciyar magajin garin mai suna Pierre David a gidan ajiye kayayyakin tarihin kasar.

A saman akwatin da aka sanya zuciyan an rubuta cewa an sanya zuciyar magajin gari “Pierre David’ a cikin akwatin nan a ranar 25 ga watan Yunin shekarar 1883.

Pierre David, wanda aka bayyana a matsayin mutumin da ya kirkiro ma'aikatar kashe gobarar garin ya mutu yana da shekara 68 ta hanyar faduwa.


News Source:   ()