Masana ilimin kayayyakin tarihi sun tono wani mutum-mutumin kunkuru mai shekaru arua-aru a tafkin Angkor.
An bayyana cewar mutum-mutumin kunkurun mai girman tsayin sentimita 56 da fadin santimita 93 ya kasance tun na lokacin karni na goma.
An kuma bayyana cewa an yi amfani dashi a wani gurin ibada da a yanzu ake kira Srah Srang a tafkin Angkor dake kasar Combodia.
Shugaba masana kayayyakin tarihin yankin Apsara watau Mao Sokny ya bayyana cewa an fara aikin tonon ne tun daga ranar 16 ga watan Maris.