An sanar da gano akwatunan gawa mai shekaru dubu biyu da dari biyar a kasar Misira.
Ma'aikatar harkokin kayayyakin tarihin kasar ta sanar da cewa an gano akwatunan gawa 3 a aikin tonon da aka gudanar a yammacin babban birnin kasar Alkahira mai tsawon mita 10 zuwa 12 da aka yi da katako mai kala-kala.
A yayin taron bayyanar da ganowar baya ga Ministan kayayyakin tarihin kasar Misira Halid Al-Anini jakadu kasashen waje 60 da kusan manema labarai 200 suka halarci taron.
Minista Anini ya bayyana cewa akwatin da aka gano da kyawaonsa ana ganin na lokacin karni na 6 da na 7a lokacin Fir'auna na 26.
Anani ya kara da cewa baya ga akwatunan gawan akwai wasu mutum-mutumi na tagulla da aka tono.