Ƴan tawayen Syria sun kifar da gwamnatin Al-Assad

Ƴan tawayen Syria sun kifar da gwamnatin Al-Assad

Shekaru 13 da suka gabata ne dai aka sha bata-kashi tsakanin gwamnatin ƙasar da ƴan tawaye, dai-dai lokacin da ake fama da girgizar ƙasa a gabas ta tsakiya.

Ƴan tawayen masu iƙirarin jihadi sun kuma magance tasirin Rasha da Iran a Syria, ƙasashen da ke marawa gwamnatin Assad baya a lokutan rikice-rikice mabanbanta.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana kawo ƙarshen gwamnatin Assad a Syria a matsayin wani tabo da ƙasarsa ta yiwa Iran da ƙungiyar Hezbollah kai tsaye.

Ƴan tawayen sun ce sun kutsa babban birnin Syria, Damascus ne ba tare da alamun baza jami’ai ba.

Shaidun gani da ido sun ce dubban jama’a cikin motoci wasu kuma a ƙafa ne suka yi cincirindo a Damascus su na darawa tare da kiran cewa sun samu ƴanci daga mulkin shekaru 50 na zuri’ar Assad.

Ƴan tawayen sun saki dubban fursoni da gwamnatin Syria ta tsare a gidan yari .

Kwamandan ƴan tawayen Abu Mohammed al-Golani ya ce babu gudu ba ja da baya kan aniyarsu ta yaƙar gwamnati da suka fara tun shekarar 2011.

Rasha wadda ke goyon bayan gwamnatin Syria, ta ce Assad ya bar ƙasar ne bayan cimma yarjejeniya da ƴan tawayen, kuma an umarce shi ya miƙa mulki cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce mulkin kama karya ya ƙare, ya kuma jinjinawa ƴan Syria.

Tun a ranar 27 ga watan Nuwamba ne kungiyar ‘yan tawaye Hayat Tahrir al-Sham da kawayenta suka fara kai farmaki ba ƙaƙƙutawa, inda suka kwace yankunan kasar daga hannun gwamnati da suka hada da manyan biranen Aleppo da Hama da Homs tare da shiga Damascus babban birnin kasar da sanyin safiyar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)