Ƴan tawayen Abzinawa a Mali sun ɗaga tutar Ukraine bayan galaba kan Wagner

Ƴan tawayen Abzinawa a Mali sun ɗaga tutar Ukraine bayan galaba kan Wagner

Bayanai sun ce mayaƙan na Wagner da kansu sun sanar da tafka gagarumar asara a karawar da suka yi da dakarun na Tuwareg da yammacin jiya Lahadi.

Kafin gumurzun sai da mayaƙan awaren na Tuareg suka gudanar da ƙwaƙwaran bincike da tattara bayanai waɗanda suka yi amfani da shi don afkawa dakarun da kuma samun gagarumar nasara a kansu.

Faya-fayan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, sun nuna yadda tarin ƴan tawayen na Tuareg suke tattaka tutar ƙasar Rasha tare da ɗaga tutar Ukraine.

A baya-bayan nan mayaƙan na Wagner na ci gaba da samun nasarori a ƙasashen Afrika da Rasha ke samun karɓuwa, abinda ya sanya wannan nasara ta mayaƙan na Turage ta gigita dakarun na Wagner.

Alamu na nuna cewa Ukraine na amfani da wani sabon salo wajen yaƙi da Rahsa da kuma tura sojojinta zuwa  ƙasashen da take ganin Rasha na da tasiri, inda a baya-bayan nan aka hango yadda sojojinta ke hada kai da ƴan tawayen Syria wajen yaki da sojojin na Wagner.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)