An sanar da tarar da mutum 4 a mace a asibitin garin Potsdam dake kasar Jamus.
Lamarin ya afku ne a asibitin garin Potsdam dake kula da lafiyar nakasassu mai nisan kilomita 30 daga Berlin babban birnin kasar.
A yayinda motocin kiwon lafiya da yan sanda suka kewaye asibitin tuni dai an fara bincike akan lamarin.
A yayinda aka tarar da matattun mutane hudu an kuma ga mutum daya da raunuka da dama.
An dai kame wata mata mai shekaru 51 da ake zargin ta kaiwa asibitin hari.