An sanar da cewa a jihar Alabama dake kasar Amurka an bindige wasu mutum 7 har lahira a cikin gidansu.
Dangane ga bayanan da suka fito daga kafafen yada labaran kasar a garin Morgan dake jihar Alabama makota sun ji karar bindiga inda suka sanar da hukumar 'yan sanda nan take.
Sai dai 'yan sandan sun tarar da mutum 7 mace bayan bindigesu da wasu suka yi.
Tuni dai am fara bincike akan lamarin
Kawo yanzu dai ba'a bayyana sunayen wadanda aka kashen ba.