An tara wa Lebanon dala biliyan daya don gudanar da ayyukan jin kai a Paris

An tara wa Lebanon dala biliyan daya don gudanar da ayyukan jin kai a Paris

A lokacin da ya ke gabatar da jawabin rufe taron da ya gudana a birnin Paris a Alhamis din nan, Barrot ya ce an tarawa Lebanon zunzurutun kuɗin da suka kai dala miliyan dari 8 don samar da kayan agaji, sannan kuma aka tara gudunmuwar kayan tsaro na dala miliyan dari biyu.

A cewar ministan , Amurka ta yi alkawarin bada tallafin kusan dala miliyan dari 3, ita kuma Faransa da ta shirya taron, ta yi alkawarin dala miliyan dari.

Sauran waɗanda suka bada gudunmuwa a wajen taro, sun hada da Majalisar Dinkin Duniya da ta bada dala miliyan dari 426, Jamus ta yi alkawarin Euro miliyan 96 ga ƙasashen Lebanon da Syria yayin da Italiya ta yi alkawarin dala miliyan 10 da dubu dari 8.

Yakin da ake yi a Lebanon tsakanin mayakan Hezbollah da sojojin Isra'ila, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 2 da dari 5, ya raba mutane miliyan daya da matsugunansu sannan kuma ya taɓarɓarar da tattalin arzikin ƙasar.

Tun da farko a jawabin buɗe taron da ya gabatar, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana cewa Lebanon na tsananin buƙatar tallafi a halin da ta ke ciki don agazawa ɗimbin jama’arta da Isra’ila ta tilastawa barin muhallansu, dama su kansu yankunan da ke basu matsugunan wuci gadi waɗanda dukkaninsu ke buƙatar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)