A rahoton da ta fitar mai taken a tsayar da yaƙar ƙananan yara, ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce an samu ƙaruwar kashi 15 cikin ɗari na take haƙƙin ƙananan yara dake rayuwa a yankunan dake fama da yaƙi a duniya.
Sama da rahotanni dubu 31 kungiyar agajin ta samu a shekarar, yayin da a kowaccce rana ta karɓi rahotonni da suka kai 86 waɗanda suka haɗa da cin zarafin yara da kai musu hare-hare a makarantu.
A cewar Musa Chibwana jami’in kididdige bayanai a kungiyar agaji ta Save the children sama da yara miliyan 473 suka fuskanci wannan matsala, adadin da ya haura kaso 1 bisa 6 na yawan alummar duniya.
Wani ƙarin take haƙƙi da yaran ke fusakanta shine yadda ake hanasu samun damar isa ga tallafin jin ƙai a Falasɗinu kamar yadda rahotannni suka tabbatar. A shekarar an samu ƙaruwar kashe kuɗi a fannin soji a duniya tare da watsi da ayyukan jin ƙai na gaggawa.
Rahoton ya ce duniya ta zamewa yara wani mummunan haɗari a shekarar 2023, kuma laifukan da ake aikatawa a wuraren da ake yaƙe-yaƙe yayi muni mara misaltuwa.
A ƙasar Sudan irin waɗannan laifukan yaki sun ninka sau 5 idan aka kwatanta da na shekarar 2022 wato daga 317 zuwa 1759
Rahoton ya mayar da hankali kan halin da yara suka tsinci kansu a sassan duniya a shekarar 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI